Application Description:
Wannan wani sabon app ne da muka kirkira wanda yake dauke da cikakken bayani mai gamsarwa da sassaukar hanya wadda zaka koyi harshen turanci da kanka.
A ciki mun yi bayanin dukkan part of speech guda takwas mun yi cikakken bayani akan kowane daya tare da misalai a cikin sentence. Hakanan kuma duk kalmomi da jimlolin da muka kawo cikin harshen turanci, muna fassarawa zuwa harshen Hausa.
Mun yi bayani akan punctuation marks wato alamomin rubutu, mun kawo sama da kalma dari biyu na abubuwan da muke amfani da su yau da kullum don bunkasa vocalary din mu.
Bamu tsaya anan ba mun kawo salon magana wato idioms sama da 50 tare da karin magana kusan 30 wanda insha Allahu zamu kara fadada app din da wasu abubuwan anan gaba. Don haka duk lokacin da ka samu message din mu cewa mun yi update to ka garzaya kayi updating don cigaba da koyon turanci kana kwance daga dakinka.
Haka nan kuma mun sanya ma app din pronouncer wadda zata taimaka wajen furta kowace irin kalmar turanci. Kawai da zaran ka shiga pronouncer sai ka rubuta kalma, sentence ko phrase da kake bukatar a karanta maka.
kar ku manta ku yi reviewing kuma ku yi rating na aikin mu.
0 Comments: