Application Description:
Akwai matsalolin maza da yawa wanda yake haddasa rashin zaman lafiya a cikin aure ko kuma saki. Su ne kamar haka:
-Karya: Wasu mazan suna yi wa matayen da za su aura karya ta hanyar nuna masu cewa sun mallaki wani abun duniya wanda a zahiri kuma babu abin, ita kuma matar za ta soka tare da kwadayin samun wannan abun bayan an yi aure.
Idan macen ta je gidan mijin kuma ta sami a kasin abin da yake fada mata to dole za su samu matsala wanda daga karshe dole za ta ce ya sake ta ko kuma su zauna cikin matsala kullum.
-Rashin Kulawa: Da yawa daga cikin maza na Hausa babsa kulawa da matansu, wanda ita kuma mace babu abin da take so sama da kulawa, idan har ya zama ba ka iya kulawa da bukatar matarka kamar abin da ya shafi abinci, sutura da sauran bukatunta, to dole za su sami matsala da mijinta wanda zai iya kawo rabuwarsu.
Kulawa ta biyu kuwa ita ce, duk mace tana son a ce mijinta yana ba ta lokacinta wajen debe mata kewa, zama da ita domin jin ra’ayinta da kuma bukatunta, sannan kuma ka tabbatar mata cewa lallai kana sonta wanda hakan shima ya yi karanci a cikin maza. Wannan matsalace babba wanda rashin samun hakan yana kawo matsala sosai har a kai ga rabuwa.
– Rashin Tsafta: Duk mace tana son ta ga mijinta yana da tsafta da kuma kula da jikinshi, kamar yanda namiji yake so ya ga matarshi da tsafta kullum haka ita ma take so, amma za ka samu cewa hausawa da yawa ba su da tsafta, wasu kuma suna da ita amma ba su yi sai za su fita kasuwa ko aiki, ba dai a cikin gidansu ba, ba su yi don matansu wanda wannan shima yana kawo matsala ko kuma rabuwa.
– Cin Amana: Da yawa daga cikin maza suna ci amanar matansu ta hanyar neman matan banza wanda wasu lokutan sai ka samu cewa mace ta kama mijinta da matar banza ko a cikin gidanta ko kuma a waje wanda wannan yana kawo rabuwar aure.
– Zargi: Maza da yawa su kan yi zargin matansu a kan abin da ya zamanto su matan ba sa aikatawa, kamar neman maza, sata, ko makamancin haka wanda wannan shima yana raba aure sosai.
– Yin Aure Don Wani Dalilin Akasin Soyayya: Maza su kan yi aure don wani dalili na abin duniya, wasu mazan suna yin aure don kwadayin cewa yarinyar mahaifinta yana da abun duniya, kuma ba za su sami dammar shiga cikin wannan abin duniyar ba har sai sun auri diya a gidan. Idan an yi auren ba su sami abin da suke za to ba, to sai su sake ta. Idan kuma sun samu to za a sami matsala har a yi saki saboda matar ta san cewa kudin babanta ne. Haka kuma wasu mazan su kan yi aure don yana yin sigar mace ko kuma sha’awa wanda idan tasami lokaci a wajen ka dole za ta canza shi kuma daga wannan lokacin zai ji baya son ganin ta saboda duk abubuwan da ke daukar hankali a tare da ita yanzu babu su, to sai su fara samun matsala wanda daga karshe sai saki.
-Matsalar Iyaye: A kasar hausa, iyayen su kan ba da matsala sosai a cikin aure, misali, za ka samu cewa da miji da mata suna son junansu, amma wani lokacin za ka ga iyayen mijin sun takura a kan cewa sai ya sake ta kuma ba tare da wata hujja ba wanda za a gamsu da ita, ko kuma su takura mata har daga karshe ta gaji ta ce ma mijin sai ya sake ta, ita ma kuma iyayenta suna iya sawa sai an sake ta saboda babu dalili. -Matsalar Yan’uwa: Lokuta da yawa yan’uwan miji suna kawo matsala a aure, kamar takurawa macen, nuna mata kiyayya, yi mata sharri da sauran ire-iren wadannan wanda daga karshe sai ka ga sun rabu an kashe auren.
-Matsalar Abokai;
Mata suna da matsaloli da yawa wanda yake kawo masu rabuwar aurensu, daga cikin matsalolin ga wasu kamar haka:
- Kwadayi
- Rashin Biyayya
– Rashin Iya Kwalliya, Abinci, Magana Da Kuma Tsafta Kwalliya
– Abinci
– Iya Magana
-- Tsafta
-- Rashin Godiya
– Gasa
– Wulakanci Mata
Category: Books and Reference App
Developer: Abrahamjr
Updated : 16/01/2022.
Android V : 4.1+
App Version : 4.2
Download APK HERE (3.7MB)
0 Comments: