Application Description:
Mallam Sa'idu Haruna Kano shi ne wanda ya ke jan bakin AlQur'ani mai girma a tafsiran da marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano yake gabatarwa duk shekara a masallacin Alhaji Muhammadu Indimi da ke Damboa road, Maiduguri, Borno State - Nigeria.
Bayan shahadar da Sheikh Ja'afar ya samu a asubahin ranar jumu'a 13th April, 2007 a sakamakon gisan gillar da yan bindiga suka yi masa na harbi da harsashan bindiga, mallam Sa'idu ya ci gaba da ja wa Sheikh Dr. Muhammad Sani Rijiyar lemo baki a masallacin indimi, kana daga bisani yanzu haka yana jan baki wa Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar a masallacin Al_Furqan dake cikin birnin Kano.
Shi kuma Dr. Rijiyar lemo ya koma tafsirinsa a masallacin Gwallaga dake Bauchi State - Nigeria.
Allah Ya saka wa malamanmu da alkhairi.
Shi kuma Sheikh Ja'afar da Albani Zaria da Dan maishiyya Sokoto da aka hallaka a fagen da'awah , Allah Ya ji kansu da rahama. Ya sa aljanna ce makomarsu.
Da fatan za ku ji dadin sauraro wannan application.
Mu na fatan kuma ku sanya mu a addu'a.
Wassalam alaikum.
0 Comments: